Malam Sa'id Harun Yankaba – Maja baƙi ga Marigayi Shaikh Ja'afar Mahmud Adam, Yanzu Kuma Dr. Bashir Aliyu Umar Alfurƙan.
A iya sanina bansan wani mai Jan baƙi a fagen Tafsiri dake biya Alqur'ani a nitse tare da ratsa zuciya kamarsa ba (mutanen Maiduguri za su tabbatar da haka), hakana duk wanda yasan gwagwarmayar da Shaikh Ja'afar yayi a rayuwarsa a fagen Tafsiri ya san anyi tane tare dashi domin kuwa duk inda kaga Malam Ja'afar zai yi Tafsiri to zaka ganshi a gefansa.
Ranar da Shaikh Ja'afar yayi Khatma a Masallacin Beirut dake kano, akwai taimako na kuɗi da ake tarawa a duk sati, Mal Ja'afar yace wannan kuɗin da aka tara babu abinda ya kamata ayi dasu illa a siyawa Mal Sa'idu mota dasu kuma abinda ya faru kenan. Allahu Akbar!
Malam Saidu mutum ne mai haƙuri da kawaici sau tari Mal Ja'afar yana cewa haƙurin da Mal Sa'idu yake yi dani yafi wanda nake yi dashi. Malam ya shafe tsahon rayuwarsa kaf gurin karanta Alƙur'ani ba tare da gajiyawa ba wanda kuma har yanzu aikin kenan.
Mutane da yawa suna zuwa Tafsiri Masallacin Alfurƙan domin su saurari Ƙira'arsa mai daɗi da sauƙi gurin koyon Alƙur'ani wadda ke tuna musu Marigayi Shaikh Ja'afar (gangaran gwani mai kyawun uslubi a fagen Tafsirin Alƙur'ani).
//zuphaims.com/4/4095235
A fagen Mu'amala kuwa, iya sanina ban taɓa ganin Mu'amala tare da mutuntawa wadda ke tsakanin mai Jan baƙi da mai Tafsiri kamar irin tasa da Dr. Bashir ba.
Allah ya ƙarawa Malam Lafiya da Tsahon rai da kuma ƙwarin gwiwa don cigaba da hidimtawa Alqur'ani.
Almustpha Murtala Mansur