Sunday, May 2, 2021
Wasu haziqan matasa sunyi abunda za ayi koyi dasu
A jiya Lahadi 20 ga watan Ramadan 1442AH wanda yayi daidai da 3 ga watan Mayu 2021 wasu matasa a garin Katsina Karkashin wata cibiya mai suna "Cibiyar Khalid bin Waleed Katsina" suka shirya taron karrama da bada shaida ga dalibai da suka halarci samina ta hardace hadisai 42 cikin littafin "Araba'una Hadis" Kimanin dalibai 28 ne suka halarci wannan saminar. Taron ya samun halartar manyan malamai na garin Katsina wanda suka hada da Shugaban majalisar malamai Sheikh Surajo Mahmud Kankia, Dr Mukhtar Usman Jibiya, Dr. Aminu Usman (Abu Ammar) Dr. Muhammadu Usamatu Abbas da sauran baki da suka samu halarta an bude taro da jawabi daga bakin magatakardar kungiyar Ada'u Bara'u Muhammad inda yayi maraba da mahalarta sannan daga bisani bada takaitaccen tarihin cibiyar da kuma aikace aikacen ta da suka shafi Karantarwa, Taimakekeniya, Da'awah (Birni da qauyuka) da sauran su Bayan nan malaman da suka samu halartar taron sun tofa albarkacin bakin su inda daga baya aka raba kyaututtuka da shaida ga dalibai Daga karshe shugaban cibiyar Ahmad Balarabe Mahmud yayi jawabin rufewa
yayi godiya ga dukkan wanda ya bada gudunmwa tunda daga farko har karshe koda da shawara ne. Sannan yayi kira ga jama'a da su bada gudunmawa don cigaba da ayyukan cibiyar
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment