Monday, March 29, 2021

Kun san lokacin da Sudais ya fara jan sallah a Harami???

Yau shekara 38 da suka wuce a rana irin ta yau Shehun malami mai girma ministan Harami guda biyu (Makkah da Madina) Farfesa Abdurrahman Sudais ya fara Jan sallah a harami kamar yadda shafin Haramain Sharifain suka ruwaito


Allah ya qarawa shehun malami lafiya da nisan kwana



Thursday, March 25, 2021

Rayuwa mai albarka sai Alarammomi

 Malam Sa'id Harun Yankaba – Maja baƙi ga Marigayi Shaikh Ja'afar Mahmud Adam, Yanzu Kuma Dr. Bashir Aliyu Umar Alfurƙan. 


A iya sanina bansan wani mai Jan baƙi a fagen Tafsiri dake biya Alqur'ani a nitse tare da ratsa zuciya kamarsa ba (mutanen Maiduguri za su tabbatar da haka), hakana duk wanda yasan gwagwarmayar da Shaikh Ja'afar yayi a rayuwarsa a fagen Tafsiri ya san anyi tane tare dashi domin kuwa duk inda kaga Malam Ja'afar zai yi Tafsiri to zaka ganshi a gefansa.


Ranar da Shaikh Ja'afar yayi Khatma a Masallacin Beirut dake kano, akwai taimako na kuɗi da ake tarawa a duk sati, Mal Ja'afar yace wannan kuɗin da aka tara babu abinda ya kamata ayi dasu illa a siyawa Mal Sa'idu mota dasu kuma abinda ya faru kenan. Allahu Akbar! 


Malam Saidu mutum ne mai haƙuri da kawaici sau tari Mal Ja'afar yana cewa haƙurin da Mal Sa'idu yake yi dani yafi wanda nake yi dashi. Malam ya shafe tsahon rayuwarsa kaf gurin karanta Alƙur'ani ba tare da gajiyawa ba wanda kuma har yanzu aikin kenan. 


Mutane da yawa suna zuwa Tafsiri Masallacin Alfurƙan domin su saurari Ƙira'arsa mai daɗi da sauƙi gurin koyon Alƙur'ani wadda ke tuna musu Marigayi Shaikh Ja'afar (gangaran gwani mai kyawun uslubi a fagen Tafsirin Alƙur'ani). 


//zuphaims.com/4/4095235

A fagen Mu'amala kuwa, iya sanina ban taɓa ganin Mu'amala tare da mutuntawa wadda ke tsakanin mai Jan baƙi da mai Tafsiri kamar irin tasa da Dr. Bashir ba. 


Allah ya ƙarawa Malam Lafiya da Tsahon rai da kuma ƙwarin gwiwa don cigaba da hidimtawa Alqur'ani.


Almustpha Murtala Mansur


KU SAN WANDA ZASU YI LIMANCIN TARAWEEH A HARAMI 1442H

 DA DUMI DUMI || 

LIMAMAN DA AKA TABBATAR SUNE ZASU JAGORANCI SALLAR TARAWEEH ASHAM) NA WATAN RAMADANAN WANNAN SHEKARAR TA 1442H



1. Sheikh Abdul Rehman Al Sudais

2. Sheikh Saud Al Shuraim

3. Sheikh Abdullah Awad Al Juhany

4.  Sheikh Maher Al Muaiqly

5. Sheikh Bandar Baleelah

6. Sheikh Yasir Al Dossary


Babu bakon liman a wannan shekarar zuwa yanzu

Sunday, March 21, 2021

Alh Dikko dan Amana ya nuna amanar shi ga Katsinawa

 KIWON LAFIYA:
 Gwagwaren Katsina ya dauki nauyin marasa lafiya a yankunan Dutsinma, da Charanchi.
 Gidauniyar Gwagwaren katsina, Alh. Dr. Dikko Umar Radda, hadin  gwiwa da Danmalikin Katsina Alh. Usman Abba Jaye. Sun dauki nauyi kula da marasa lafiya 1000 a Kananan hukumomin Charanci da Dutsinma.







Shirin ya samu karbuwa daga gwamnatochi
da kuma shuwagabannin kananan hukumomin.
       Wannan dai na daga  cikin kokarin mai girma Gwagwaren Katsina, Alh. Dr. Dikko Radda wajen ganin ya inganta  rayuwar alummar yankin.

Shirin ya hada  da Bada magunguna da kuma theatre.
An ware likitoci mata don  lura da matsalolin mata, da kuma likitocin yara.

Shirin na gudana a halin yanzu a gundumar Dutsinma, kuma ana duba  marasa lafiya 300 ko wace rana.

Muhammad Isah Rawayau

Friday, March 19, 2021

Duniyar Ilimi tayi babban rashi


 Yau Juma'ah 6 ga watan Sha'aban 1442H daidai da 19 ga watan Maris 2021 Allah yayi wa babban malami masanin Alqu'ani da ilimomin sa rasuwa wato Sheikh Muhammad Ali As-Sabuni mawallafin littafin "Attibyan fi Ulumin Qura'an" 


Shehun malamin ya rasu yanada shekara 91 a duniya, kafin rasuwar shi ya koyar a Jami'ar Ummul Qura dake Saudiyya kimanin shekara 28. Ya kuma rubuta littafai da dama wanda duniyar Ilimi take amfana kuma zata cigaba da amfana dasu

Lallai wannan yana cikin alamomin tashin Alqiyama kamar yadda manzon tsira (SAW) ya fada cewa za'a dauke ilimi. Tabbas an dauke ilimi a nan

Allah ya ji qansa yasa aljanna ce makomar sa idan ajalin mu yazo Allah yasa mu cika da imani


Ahmad Balarabe Maidole 

Tuesday, March 16, 2021

NIMET Tayi sabon DG daga katsina.


 Buhari Ya Nada Farfesa Bako Matazu Sabon Shugaban Hukumar Kula Da Hasashen Yanayi Ta Nijeriya (NiMET)


Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Farfesa Bako Mansur Matazu a matsayin sabon shugaban Hukumar Hasashen Yanayi Ta Najeriya, watau Nigerian Meteorogical Agency (NiMET) inda ya maye gurbin Farfesa Sani Mashi.


Sabon Shugaban Hukumar, Farefesa Bako Mansur Matazu, dan asalin karamar hukumar Matazu ne a jihar Katsina, yana da Digiri na ukku akan hasashen yanayi kuma memba ne a kungiyoyin ƙwararru hasashen yanayi da muhalli da kuma makamashi.


Kafin nadin nasa shi ne janar manaja na hasashen yanayi da bincike na hukumar.


Allah Ya Taya Riko!

Friday, July 3, 2020

An bankado wata almundahana a gwamnatin katsina.

....Wasika daga Mahadi Shehu.

Zuwa ga Alummar Jahar Katsina, Talakawa na Birni dana karkara, Malamai, Limamai da Masarautar Katsina a cikin Shirin Barkada Warhaka na Gidan Radio Freedom Kaduna.

Kai Tsaye Mahadi Ya Bayyana cewa Yana mika Sakon shine ga Al'ummar Jahar Katsina Milyan Bakwai da Dubu Dari Takwas da Talatin da Daya da Dari Ukku (7,831,300) 

Mahadi ya Bayyana cewa Daga Shekarar Dubu Biyu da Sha Biyar zuwa Dubu Biyu da Sha Tara Gwamnatin Jahar Katsina ta Kashe Naira Milyan Dubu Ashirin da Hudu, wato Bilyan Ashirin da Hudu (24,000,000,000.00) daga Asusun kula da Tsaro na Jahar Katsina (security vote).

Yayi Bayani Dalla Dalla yadda aka Wawushe Kudin da Kuma Asusunan da aka tura Kudaden, ya Bayyana cewa Karshen watan Biyar na Shekarar Dubu Biyu da Sha Takwas an ba S.A Political kudi Naira Milyan Dari Biyar domin zuwa Conversation a Abuja.

Haka nan ya Bayyana wasu Asusunan Banki har Guda Ukku da ya Bayyana cewa an baiwa kowane daga cikin su Naira Milyan Dari da Ashirin da Biyar.

Jami'an Tsaron Yansanda:-

Kazalika An ware wasu Kudade domin bada Tsaro a wutar Lambar Rimi, zunzutun Kudi Naira Milyan Dari Shidda da Tamanin da Hudu da Dubu Dari Ukku da Talatin da Shidda da Dari Shidda domin Yansanda Kwara Goma Tsawon Shekaru Hudu.

Limamai da Malamai:- 

Bayanan sun nuna cewa a cikin Shekarar Dubu Biyu da Sha Biyar Gwamnatin da ta gabata taba Malamai kudi Naira Dubu Dari Takwas da Hamsin domin sayen Riguna, a Shekarar Dubu Biyu da Sha Shidda itama wannan Gwamnatin ta Biya su irin wadannan kudin sai dai Shekarar Dubu Biyu da Sha Bakwai abun ya Chanza domin an ware Kudi a Shekarar Dubu Biyu da Sha Bakwai Naira Milyan Dari Hudu da Chas'in da Takwas da Dubu Dari da Ashirin da Biyar da Naira Dari Biyu da Hamsin da Takwas domin sayen Riguna ga Limaman na Katsina, a Shekarar Dubu Biyu da Sha Takwas kuma an ware Naira Milyan Talatin da Shidda, sai Kuma aka ware Naira Milyan Ashirin da Biyar domin Kungiyar Izala ta Kaduna da Kuma Naira Dubu Dari Biyar domin Bangaren Izalar Jos.

Sayen Wayoyin Salular:-

Sannan Kuma an sayi Wayoyin Salula Sau Ukku Kamar haka: 

i- Naira Milyan Dari da Biyar Domin Membobin Majalisar Tsaro na Jahar nan

ii- Naira Milyan Dari Ukku da Goma Sha Hudu Domin Chairmomin Kananan Hukumomin Jahar nan na rukon Kwarya

iii- Naira Milyan Dari da Sha Hudu Domin Yan Majalisar Jahar nan

Masarautar Katsina:-

Mahadi ya Bayyana cewa An ware ma Masarautar Katsina Naira Milyan Dari da Sittin da Biyar domin Ran Gadi zuwa Dajin Rugu.

Haka nan an sake ware wasu kudin Naira Milyan Talatin da Biyar  domin yin Taron Tsaro duk da sunan Masarautar Katsina.

Mahadi ya Bayyana cewa a cikin Watan Sha Daya na Shekarar Dubu Biyu da Sha Bakwai wani Babban Jami'an tsaro yazo Jahar Katsina an ware kudi Naira Milyan Dari Biyu da Hamsin an bashi kyauta.

Haka nan an ware Naira Milyan Dari da Saba'in an Baiwa Jami'an tsaron Gidan Gwamnatin da sunan welfare.

Mahadi ya Bayyana cewa zuwa Karshen watan da yagaba Tarin Maaikatan da sukayi Ritaya a fadin Jahar nan zasu kai Mutane Dubu Ashirin da Biyar kuma suna bin bashin Fanshon su na yawan Naira Bilyan Goma Sha Biyu, ya Kara da Cewa Yanzu Jahar Katsina tana fama da Bashin Naira Bilyan Chas'in da Shidda akan ta.

Mahadi yache duk Abubuwan da ya fadi yanada Hujjoji akansu Idan an tsakureshi zai bada, yama kara da Cewa Akwai Badakalar kashe Kudaden da akayi da bai Bayyana ba Kimanin Dari da Goma Sha Takwas wadanda bai Bayyana ba sai zuwa nan gaba idan Lokachin yin hakan yayi, ya kuma che Idan ya Bayyana su wannan da ya Bayyana kamar wasan Yara ne.

Daga Muhammad Aminu Kabir.

Friday, June 26, 2020

N-Power is taking in new beneficiaries

Unemployed Graduates to serve as Npower Beneficiaries




Graduates of Bachelor Degree, HND, OND and NCE are called to apply for the Npower programme which is going to be open today, 26th June, 2020 by 11:45pm.

This was published on the Npower Twitter handle Yesterday 25th June, 2020. The statement read thus:

"Are you unemployed and between the ages of 18-35? Do you want to contribute in building a skilled Nigerian workforce?

Apply for N-Power!"

"Since 2016, the Nigerian Govt. has upskilled over 500,000 beneficiaries through N-Power".