Sunday, May 2, 2021
Wasu haziqan matasa sunyi abunda za ayi koyi dasu
A jiya Lahadi 20 ga watan Ramadan 1442AH wanda yayi daidai da 3 ga watan Mayu 2021 wasu matasa a garin Katsina Karkashin wata cibiya mai suna "Cibiyar Khalid bin Waleed Katsina" suka shirya taron karrama da bada shaida ga dalibai da suka halarci samina ta hardace hadisai 42 cikin littafin "Araba'una Hadis" Kimanin dalibai 28 ne suka halarci wannan saminar. Taron ya samun halartar manyan malamai na garin Katsina wanda suka hada da Shugaban majalisar malamai Sheikh Surajo Mahmud Kankia, Dr Mukhtar Usman Jibiya, Dr. Aminu Usman (Abu Ammar) Dr. Muhammadu Usamatu Abbas da sauran baki da suka samu halarta an bude taro da jawabi daga bakin magatakardar kungiyar Ada'u Bara'u Muhammad inda yayi maraba da mahalarta sannan daga bisani bada takaitaccen tarihin cibiyar da kuma aikace aikacen ta da suka shafi Karantarwa, Taimakekeniya, Da'awah (Birni da qauyuka) da sauran su Bayan nan malaman da suka samu halartar taron sun tofa albarkacin bakin su inda daga baya aka raba kyaututtuka da shaida ga dalibai Daga karshe shugaban cibiyar Ahmad Balarabe Mahmud yayi jawabin rufewa
yayi godiya ga dukkan wanda ya bada gudunmwa tunda daga farko har karshe koda da shawara ne. Sannan yayi kira ga jama'a da su bada gudunmawa don cigaba da ayyukan cibiyar
Tuesday, April 20, 2021
Mata 1500 ne zasu taimaki masu umrah mata a Harami
Monday, April 12, 2021
Daren farko na Ramadan 1442
Yadda aka gudanar da sallar taraweeh (Asham) a haramin Makkah daren farko na Ramadan 1442
Alhamdulillah
Friday, April 9, 2021
LABARI MAI DUMI MAI DADI DAGA HARAMI
Jerin Limamai da zasu jagoranci sallar Taraweeh (Asham) a Masallacin manzo (S.A.W)
#Ramadan1442
1. Sheikh Ahmed Talib / Sheikh Abdullah Buayjan
2. Sheikh Khalid Muhanna / Sheikh Ahmed Hudaify
3. Sheikh Abdul Muhsin Qasim / Sheikh Salah Budayr
Sheikh Ali Hudaify ana tunanin ba zai ja sallar taraweeh ba wannan shekarar
Wednesday, April 7, 2021
Alheri danqo ne
Masallacin kenan da jaruma Hadiza Gabon ta gina Fisabilillahi kamar yadda ta bayyana hakan a shafinta na Facebook
Wane fata zakuyi mata???
Monday, April 5, 2021
Kafin Ramadan 1442
Sheikh Sa'ud Shuraim zai jagoranci sallar magriba da isha' yau litinin 23 ga watan Sha'aban 1442 sai kuma wani lokaci inshaAllah
Haramain Sharifain
Abubuwa sun daidaita
An samu sasanci tsakanin bankuna da kamfanin layi
Yanzu haka zaku iya sanya kati ko wani abu mai kama da haka daga bankunan ku ta hanyar amfani da wayoyin hannun ku
Monday, March 29, 2021
Kun san lokacin da Sudais ya fara jan sallah a Harami???
Yau shekara 38 da suka wuce a rana irin ta yau Shehun malami mai girma ministan Harami guda biyu (Makkah da Madina) Farfesa Abdurrahman Sudais ya fara Jan sallah a harami kamar yadda shafin Haramain Sharifain suka ruwaito
Allah ya qarawa shehun malami lafiya da nisan kwana
Thursday, March 25, 2021
Rayuwa mai albarka sai Alarammomi
Malam Sa'id Harun Yankaba – Maja baƙi ga Marigayi Shaikh Ja'afar Mahmud Adam, Yanzu Kuma Dr. Bashir Aliyu Umar Alfurƙan.
A iya sanina bansan wani mai Jan baƙi a fagen Tafsiri dake biya Alqur'ani a nitse tare da ratsa zuciya kamarsa ba (mutanen Maiduguri za su tabbatar da haka), hakana duk wanda yasan gwagwarmayar da Shaikh Ja'afar yayi a rayuwarsa a fagen Tafsiri ya san anyi tane tare dashi domin kuwa duk inda kaga Malam Ja'afar zai yi Tafsiri to zaka ganshi a gefansa.
Ranar da Shaikh Ja'afar yayi Khatma a Masallacin Beirut dake kano, akwai taimako na kuɗi da ake tarawa a duk sati, Mal Ja'afar yace wannan kuɗin da aka tara babu abinda ya kamata ayi dasu illa a siyawa Mal Sa'idu mota dasu kuma abinda ya faru kenan. Allahu Akbar!
Malam Saidu mutum ne mai haƙuri da kawaici sau tari Mal Ja'afar yana cewa haƙurin da Mal Sa'idu yake yi dani yafi wanda nake yi dashi. Malam ya shafe tsahon rayuwarsa kaf gurin karanta Alƙur'ani ba tare da gajiyawa ba wanda kuma har yanzu aikin kenan.
Mutane da yawa suna zuwa Tafsiri Masallacin Alfurƙan domin su saurari Ƙira'arsa mai daɗi da sauƙi gurin koyon Alƙur'ani wadda ke tuna musu Marigayi Shaikh Ja'afar (gangaran gwani mai kyawun uslubi a fagen Tafsirin Alƙur'ani).
//zuphaims.com/4/4095235
A fagen Mu'amala kuwa, iya sanina ban taɓa ganin Mu'amala tare da mutuntawa wadda ke tsakanin mai Jan baƙi da mai Tafsiri kamar irin tasa da Dr. Bashir ba.
Allah ya ƙarawa Malam Lafiya da Tsahon rai da kuma ƙwarin gwiwa don cigaba da hidimtawa Alqur'ani.
Almustpha Murtala Mansur
KU SAN WANDA ZASU YI LIMANCIN TARAWEEH A HARAMI 1442H
DA DUMI DUMI ||
LIMAMAN DA AKA TABBATAR SUNE ZASU JAGORANCI SALLAR TARAWEEH ASHAM) NA WATAN RAMADANAN WANNAN SHEKARAR TA 1442H
1. Sheikh Abdul Rehman Al Sudais
2. Sheikh Saud Al Shuraim
3. Sheikh Abdullah Awad Al Juhany
4. Sheikh Maher Al Muaiqly
5. Sheikh Bandar Baleelah
6. Sheikh Yasir Al Dossary
Babu bakon liman a wannan shekarar zuwa yanzu
Sunday, March 21, 2021
Alh Dikko dan Amana ya nuna amanar shi ga Katsinawa
Gwagwaren Katsina ya dauki nauyin marasa lafiya a yankunan Dutsinma, da Charanchi.
Gidauniyar Gwagwaren katsina, Alh. Dr. Dikko Umar Radda, hadin gwiwa da Danmalikin Katsina Alh. Usman Abba Jaye. Sun dauki nauyi kula da marasa lafiya 1000 a Kananan hukumomin Charanci da Dutsinma.
Shirin ya samu karbuwa daga gwamnatochi
da kuma shuwagabannin kananan hukumomin.
Wannan dai na daga cikin kokarin mai girma Gwagwaren Katsina, Alh. Dr. Dikko Radda wajen ganin ya inganta rayuwar alummar yankin.
Shirin ya hada da Bada magunguna da kuma theatre.
An ware likitoci mata don lura da matsalolin mata, da kuma likitocin yara.
Shirin na gudana a halin yanzu a gundumar Dutsinma, kuma ana duba marasa lafiya 300 ko wace rana.
Muhammad Isah Rawayau
Friday, March 19, 2021
Duniyar Ilimi tayi babban rashi
Yau Juma'ah 6 ga watan Sha'aban 1442H daidai da 19 ga watan Maris 2021 Allah yayi wa babban malami masanin Alqu'ani da ilimomin sa rasuwa wato Sheikh Muhammad Ali As-Sabuni mawallafin littafin "Attibyan fi Ulumin Qura'an"
Shehun malamin ya rasu yanada shekara 91 a duniya, kafin rasuwar shi ya koyar a Jami'ar Ummul Qura dake Saudiyya kimanin shekara 28. Ya kuma rubuta littafai da dama wanda duniyar Ilimi take amfana kuma zata cigaba da amfana dasu
Lallai wannan yana cikin alamomin tashin Alqiyama kamar yadda manzon tsira (SAW) ya fada cewa za'a dauke ilimi. Tabbas an dauke ilimi a nan
Allah ya ji qansa yasa aljanna ce makomar sa idan ajalin mu yazo Allah yasa mu cika da imani
Ahmad Balarabe Maidole
Tuesday, March 16, 2021
NIMET Tayi sabon DG daga katsina.
Buhari Ya Nada Farfesa Bako Matazu Sabon Shugaban Hukumar Kula Da Hasashen Yanayi Ta Nijeriya (NiMET)
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Farfesa Bako Mansur Matazu a matsayin sabon shugaban Hukumar Hasashen Yanayi Ta Najeriya, watau Nigerian Meteorogical Agency (NiMET) inda ya maye gurbin Farfesa Sani Mashi.
Sabon Shugaban Hukumar, Farefesa Bako Mansur Matazu, dan asalin karamar hukumar Matazu ne a jihar Katsina, yana da Digiri na ukku akan hasashen yanayi kuma memba ne a kungiyoyin ƙwararru hasashen yanayi da muhalli da kuma makamashi.
Kafin nadin nasa shi ne janar manaja na hasashen yanayi da bincike na hukumar.
Allah Ya Taya Riko!